Isa ga babban shafi
FIFA

"Gasar Qatar 2022 ba za ta yi karo da Olympics ba"

Shugabar shirya gasar cin kofin duniya Thomas Bach ya yi alkawalin cewa gasar kwallon kafar ta 2022 da ake cece kuce akai da Qatar za ta dauki nauyi ba zai yi karo da wasannin Olympics ba da ake gudanarwa a lokacin hunturu.

Joseph Blatter, Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA
Joseph Blatter, Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA REUTERS/Steve Christo
Talla

Hukumar FIFA tace a lokacin sanyi ne za a gudanar da gasar saboda matsanancin zafi a Qatar, amma wasu na ganin gasar za ta yi karo da wasannin Olympics.

Tuni dai kasashen Turai ke koken cewa dage wasannin zuwa lokacin sanyi zai shafi wasanninsu na kwallon kafa.

Sai dai har yanzu FIFA bata sanar da sabon lokacin gudanar da wasannin ba a Qatar sabanin watan Yuni da aka saba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.