Isa ga babban shafi
Premier League

Liverpool ta casa Everton, United ta doke Cardiff

Juan Mata ya shiga Old Trafford da kafar dama inda a haskawar shi ta farko Manchester United ta doke Cardiff City ci 2-0 a wasannin Premier, yayin da kungiyar Liverpool ta caccasa Everton ci 4-0 a filin wasa na Anfield.

Sabon dan wasan Manchester United  Juan Mata tare da Robin van Persie a karawarsu da Cardiff City a gasar Premier
Sabon dan wasan Manchester United Juan Mata tare da Robin van Persie a karawarsu da Cardiff City a gasar Premier REUTERS/Darren Staples
Talla

Juan Mata da shi David Moyes ya fara wasa a Old Trafford wanda ya sayo daga Chelsea.

Robin van Persie da Wayne Rooney dukkaninsu sun haska a wasan bayan sun dawo daga jinyar rauni.

Kungiyar Arsenal kuma da ke jagorancin teburin Premier ta yi barin maki ne a jiya Talata bayan Southampton ta rike ta ci 2-2.

Kungiyar Liverpool ta caccasa Everton ne ci 4-0 a filin wasa na Anfield. Steven Gerrard da Luis Suarez da Daniel Sturridge ne suka zirawa Liverpool kwallayenta a ragar Everton.

Yanzu Liverpool da ke matsayi na hudu a Premier ta ba Tottenham ne tazarar maki 3 sannan kuma ta ba Everton maki 4 wadanda ke hamayya da Liverpool wajen neman shiga wasannin gasar zakarun Turai.

A yau Laraba ne Tottenham zata karbi bakuncin Manchester City.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.