Isa ga babban shafi
Wasanni

An bai wa Ronaldo lambar yabo mafi girma a kasar Portigal

A birnin Lisbon na kasar Portigal a jiya litinin shugaban kasar Anibal Cavaco Silva da kansa ya jagoranci bikin bayar da lambar girmamawa mafi girma a kasar ga Cristiano Ronaldo dan wasan Real Madrid wanda ya samu kyautar yabo ta shahrarren dan kwallon kafa na Ballon D’or a makon da ya gabata.

Cristiano Ronaldo da shugaban Portigal Cavaco Silva
Cristiano Ronaldo da shugaban Portigal Cavaco Silva http://www.presidencia.pt/
Talla

An dai gudanar da bikin ne a cikin fadar shugaban kasar, inda aka bai wa Ronaldo wannan lamba mai suna The Order of Prince Henry.

Shugaba Anibal, ya jinjinawa Ronaldo tare da bayyana shi da cewa mutum ne da ya taka kuma yake kan taka rawa domin daukaka sunan Portigal a duniya baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.