Isa ga babban shafi
Tennis

Del Potro ya lashe kyautar Gwarzon Argentina

Dan wasan Tennis Juan Martin del Potro ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Argentina inda ya doke Dan wasan Barcelona Lionel Messi wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya sau hudu. Del Potro wanda shi ne na Biyar a duniyar Tennis, ya taba lashe kofin US Open a 2009.

Dan wasan Tennis Juan Martin Del Potro na Argentina yana a lokacin da ya doke Roger Federer a london
Dan wasan Tennis Juan Martin Del Potro na Argentina yana a lokacin da ya doke Roger Federer a london © Reuters
Talla

A shafin dan wasan na Facebook, Del potro ya bayyana farin cikin shi ga wannan kyautar zinarin da ya karba.

Del Potro shi ne ya buga wasan kusa da karshe tsakanin shi da Novak Djokovic a Wimbledon, a wasa mafi tsawon lokaci da aka kwashe a tarihin gasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.