Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

City ta doke Milan a Allianz Arena

Manchester City ta doke AC Milan a gasar lashe kofin Audi ci 5-3 a filin wasa na Allianz Arena. Minti uku da fara wasa ne David Silva ya fara bude raga, kafin minti 19 kuma City ta sake zira kwallo ta biyu.

Micah Richards yana murnar zira kwallo a ragar AC Milan tare da abokan wasan shi na Manchester City a wasan sada zumunci na neman lashe kofin Audi a Jamus
Micah Richards yana murnar zira kwallo a ragar AC Milan tare da abokan wasan shi na Manchester City a wasan sada zumunci na neman lashe kofin Audi a Jamus REUTERS/Michaela Rehle
Talla

Sai da Manchester City ta zira kwallaye biyar a raga kafin Stephan El Shaarawy da Andrea Petagna su ramawa AC Milan kwallaye biyu a raga.

Tuni dai Bayern Munich ta doke kungiyar Sao Paulo ta Brazil ci 2-0, kuma a wasan karshe za’a kara ne tsakanin yaran Pep Guardiola na Bayern Munich da ‘yan wasan Manuel Pellegrini na Manchester City.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.