Isa ga babban shafi
Copa Del Ray

Barcelona ta sha kashi a hannun Real Madrid

Real Madrid ta bi Barcelona har gida ta lallasa ta ci 1-3 a Nou Camp wanda hakan ya ba Madrid nasarar zuwa buga wasan karshe a gasar Copa Del Ray. Cristiano Ronaldo ne ya zira kwallaye biyu a ragar Barcelona, daga nan kuma Raphael Varane ya zira kwallo ta uku a raga ana saura minti 22 a kammala wasa.

Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya dafe fuska bayan sun sha kashi a hannun Real Madrid a filin wasa na Nou Camp a gasar Copa Del Ray
Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya dafe fuska bayan sun sha kashi a hannun Real Madrid a filin wasa na Nou Camp a gasar Copa Del Ray REUTERS/Albert Gea
Talla

Jordi Alba ne ya samu damar zirawa Barcelona kwallo daya ana mintinan karshe a kammala wasa.

Yanzu Real Madrid za ta kara ne tsakaninta da Sevilla ko Atletico Madrid wadanda za su kara a yau Laraba.

Bayan zira kwallaye biyu a daren jiya, kwallaye shida ke nan Ronaldo ya zira a ragar Barcelona a wasan Classico.

A karshen mako ne kuma kungiyoyin biyu za su sake kece raini da juna a La liga inda Barcelona ke saurarutar teburin gasar da tazarar maki 16 tsakaninta da abokiyar hamayyarta Real Madrid.

Faransa

Saint-Etienne ta doke Lille 3-2 a gasar neman lashe kofin kasar wanda hakan kuma ya ba Saint-Etienne naarar tsallakewa zuwa zagayen Kwata fainal.

A yau ne kuma Paris Saint-Germain za ta sake kece raini da abokiyar hammayarta Marseille, bayan PSG ta doke ta ci 2-0 a karshen mako.

Ana tunanin Kocin PSG Carlo Ancelotti zai sako David Beckham a wasan bayan ajiye shi a benci a karshen mako.

Jamus

A gasar cin kofin kasar Jamus, Mainz ta sha kashi ci 3-2 a hannun Freiburg. A yau Laraba ne kuma Bayern Munich za ta kece raini da Borussia Dortmund.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.