Isa ga babban shafi
Champions League

Akwai sauran aiki, inji Mourinho da Ferguson

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya ce akwai sauran aiki a gaban shi kafin sanin makomar Real Madrid bayan sun tashi wasa kunnen doki ci 1-1 da Manchester United a Bernabeu. A Ranar 5 ga watan Maris ne Mourinho zai kai wa Ferguson ziyara a Old Trafford.

Jose Mourinho na Real Madrid da Sir Alex Ferguson na Manchester United
Jose Mourinho na Real Madrid da Sir Alex Ferguson na Manchester United REUTERS/Sergio Perez
Talla

Manchester United tana da kwarin gwiwa saboda kwallon da Danny Welbeck ya zira a ragar Madrid. Amma akwai kalubale idan Real Madrid ta zira kwallaye a ragar United a Old Trafford.

Mourinho wanda ya lashe kofin gasar Zakarun Turai a FC Porto da Inter Milan yace dole sai sun nemi zira kwallo a gidan Manchester.

“Dole sai mun zira kwallo a Old Trafford, kungiyoyi da dama sun yi haka”, inji Mourinho.
Sakamakon wasan ya yi wa Sir Alex Ferguson dadi tare da jinjinawa ‘Yan wasan shi musamman Golan United, David De Gea da Welbeck da kuma Phil Jones.

“Duk da yake ban ji dadin yadda muka buga wasan ba kafin hutun rabin lokaci, amma samun zira kwallo a raga abu ne mai muhimmaci. Ba a gama wasa ba amma muna da kwarin giwar tsallakewa” inji Ferguson.

A daya bangaren kuma Borussia Dortmund ta samu nasarar zira kwallaye biyu a ragar Shakhtar Donetsk inda aka tashi wasan ci 2-2 a Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.