Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Emenike ya lashe kyautar Dan wasan da ya fi zira kwallaye a raga

Dan wasan Najeriya Emmanuel Amenike ya lashe kyautar Dan wasan da ya fi zira kwallaye a gasar ta cin kofin Nahiyar Afrika wacce aka kammala a jiya, inda ya samu kwallaye hudu. A wani bangaren kuma Dan wasan tsakiya na kasar Burkina Faso, Jonathan Pitroipa ne aka zaba a matsayin dan wasan da yafi haskawa a gasar. Pitroipa dai yana bugawa club din Rennes ne a kasar Faransa.  

Dan wasn Najeriya, Emmnuel Emenike
Dan wasn Najeriya, Emmnuel Emenike rfihausa
Talla

A wani bangaren tarihin gasar, wannan ta wacce aka fara ta a ashekarar 1975, kasar Masar ce tafi kowace kasa lashe wannan gasa, inda ta samu nasara sau bakwai, sannan sai kasashen Kamaru da Ghana inda suka lashe sau hudu-hudu a yayin da Najeriya ta lashes sau uku.

Har ila yau kasar Zaire, wato Janhuriyar Demokradiyar Congo a yanzu, sau biyu ta lashe gasar, sannan kasashen Algeria, Congo Brazaville, Cote d’ Ivoir Morocco da Afrika ta Kudu da Sudan har ila yau da Tunisia da Zambia suka lashe sau daya-daya.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.