Kwallon kafa
Messi ya sabunta kwantirakinsa da Barcelona
Dan wasan Barcelona, Lionel Messi ya bi sahun Carles Puyol da Xavi Hernandez wajen sabunta kwantirikinsu da kungiyar, wanda haka zai ba shi damar zama a Barcelona har nan da zuwa karshen watan Yunin shekarar 2018.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Da ma a watan Dismbar bara ne club din ta bayyana cewa Messi zai sabunta kwantirakin na sa wanda zai kare a shekarar 2016.
Yanzu haka Messi na da kwallaye 34 a wasanni 22 da ya buga a wannan kakar wasa, kuma har ila yau shine ya lashe kyautar gwarzon kwallon kafar duniya na shekarar 2012 a karo na hudu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu