Isa ga babban shafi
FIFA

Lionel Messi ne Gwarzon Duniya

Dan wasan Argentina Lionel Messi na Barcelona shi ne Hukumar FIFA ta zaba gwarzon dan wasan Duniya na bana wanda ya ba shi damar kafa tarihi a matsayin dan wasa na farko da ya lashe kyautar karo hudu a jere da jere.

Dan wasan Barcelona, Lionel Messi rike da Kyautar gwarzon dan wasan Duniya da ya lashe karo na hudu a jere
Dan wasan Barcelona, Lionel Messi rike da Kyautar gwarzon dan wasan Duniya da ya lashe karo na hudu a jere REUTERS/Michael Buholzer
Talla

Messi dai ya samu rinjayen kuri’u ne kashi 41.60 fiye da abokan Takarar shi Cristiano Ronaldo na Real Madrid wanda ya samu kuri’u 23.68 da kuma Iniesta a matsayi na uku da kuri’u 10.91.

A bara ne dai Messi ya yi kafada da Michel Platini a matsayin ‘yan wasan da suka taba lashe kyutar sau uku a jere, da kuma Johan Cruyff da Marco Van Basten da suka lashe kyautar sau uku.

Kocin Spain ne Vicente del Bosque shi ne ya lashe kyautar gwarzon Koci bayan samun kuri’u fiye da Mourinho na Real Madrid da kuma tsohon Kocin Barcelona Pep Guardiola.
Bayan lashe kyautar Messi yace zai yi murna ne tare da abokan wasan shi musamman Andres Iniesta. Wanda suka kai ziyara tare a birnin Zurich.

A nasa bangaren kuma duk da Andres Iniesta bai samu lashe kyautar ba amma yace ko a badi yana ganin Messi ne zai lashe kyautar domin shi ke da yawan kwallaye a La liga tare da karya tarihin Mueller bayan ya zira kwallaye 91 a raga a shekara.

FIFA dai ta zabi ‘yan wasan Real Madrid guda biyar ne da ‘yan wasan Barcelona Biyar tare da Rademel Falcao a mastayin ‘yan wasan hukumar na bana.

A bangaren mata kuma ‘yar kasar Amurka ce Abby Wambach ita ce FIFA ta zaba Jarumar kwallon kafa a karon farko wacce ta zira kwallaye Biyar a raga a wasannin Olympics wanda kuma ya ba Amurka nasarar lashe zinari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.