CAF
Hukumar CAF za ta zabi gwarzon Afrika
Hukumar CAF da ke kula da kwallon kafa a Nahiyar za ta zabi gwarzon dan wasan Afrika tsakanin ‘Yan wasan Cote d’voire guda biyu Didier Drgba da Yaya Toure da kuma dan wasan Kamaru Alexendre Song.
Wallafawa ranar:
Talla
Drogba dai shi ne ya taimakawa Chelsea lashe kofin zakarun Turai karo na farko yayin da kuma Yaya Toure mai rike da kambun ya lashe kofin Premier a Manchester City.
Wannan ne kuma karon farko da hukumar CAF ta zabi Alex Song domin ba shi kyautar bisa irin rawar da ya taka a Arsenal kafin ya koma taka kwallo a Barcelona.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu