Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Lampard ya ceto Ingila, Van Persie ya samu rauni

A wasannin neman shiga gasar cin kofin Duniya da aka gudanar a jiya Talata a kasashen Turai, a filin wasa na Wembley, wasa tsakanin Ingila da Ukraine an tashi ne kunnen doki ci 1-1 kuma Frank Lampard ne ya taimakawa Ingila zira kwallo a raga, sai dai kafin kammala wasan alkalin wasa ya ba Steven Gerrard jan kati.

Dan wasan Holland Robin van Persie  a lokacin da ya samu rauni a wasa neman shiga gasar cin kofin Duniya tsakanin Holland da Hungary
Dan wasan Holland Robin van Persie a lokacin da ya samu rauni a wasa neman shiga gasar cin kofin Duniya tsakanin Holland da Hungary REUTERS/Laszlo Balogh
Talla

Kasar Italia kuma ta lashe wasanta na farko a fafatawar neman shiga gasar cin kofin Duniya, inda a jiya ta doke Malta ci 2-0 a birnin Modena. Mattia Destro da Federico Peluso ne suka zirawa Italia kwallayenta a raga.

Dan wasan Valencia ne kuma Roberto Saldado ya taimakawa Spain doke Georgia ci 1-0.

Kasar Belarus kuma tasha kashi ne hannun Faransa ci 3-1.

Kasar Holland kuma ta doke Hungary ci 4-1 a birnin Budapest. Sai dai dan wasan Manchester United Robin Van Persie bai sha da dadi ba domin ya fice wasan saboda rauni.

Kasar Romania ta doke Andorra ne ci 3-0. Kamar yadda kasar Jamus ta lallasa Austria ci 2-1. Marco Reus da Mesut Ozil su ne suka zirawa kasar Jamus kwallayenta biyu a raga. Yayin da kuma Zlatko Junuzovic ya zira wa Austria kwallonta daya a ragar Jamus
A birnin Istanbul kuma kasar Turkiya ta lallasa Estonia ci 3-0. Kasar Rasha kuma ta doke Isra’ila ci 4-0.

Kasar Azerbaijan kuma ta sha kashi ne hannun Portugal ci 3-0.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.