Isa ga babban shafi
Tennis

Serena ta lashe US open bayan doke Azerenka

Serena Williams ce ta lashe gasar US Open a bangaren mata bayan ta doke jarumar Tennis ta duniya Victoria Azerenka. Wannan ne karo na hudu da Serena William ke lashe US Open, kuma karo na 15 ke nan tana lashe Grand Slam.

Venus Williams 'Yar kasar Amurka rike da kofin da ta lashe a gasar US Open bayan doke Azarenka ta Belarus
Venus Williams 'Yar kasar Amurka rike da kofin da ta lashe a gasar US Open bayan doke Azarenka ta Belarus REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Serena ce ta lashe US Open a shekarar 1999 da 2002 da kuma 2008, sannan ta lashe French Open ta Rolland Garros a 2002 tare da lashe Austalian Open sau biyar da Wimbledon sau biyar.

A bangaren maza kuma a yau ne Novak Djokovic mai rike da kofin gasar zai kare kambunsa inda zai fafata da Andy Murray na Birtaniya wanda ya lashe Zinari a wasannnin Olympics.

Duk dai wanda ya lashe gasar tsakanin Novak Djokovic da andy Murray zai karbi kudi kusan Dala Miliyan uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.