Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Madrid da Milan sun sha kashi, Van Persie ya haska a Old Trafford

Real Madrid ta sha kashi ci 2-1 a gidan Getafe a La liga bayan ta yi kunnen doki ci 1-1 da Velencia a wasan farko. Yanzu kuma maki biyar ne tsakaninta da Barcelona wacce ta sha da kyar hannun Osasuna.

Robin van Persie, Sanye da rigar Manchester United
Robin van Persie, Sanye da rigar Manchester United REUTERS/Phil Noble
Talla

Gonzalo Higuain ne ya fara zirawa Madrid kwallo a raga ana minti 26 da fara wasa amma bayan dawowa hutun rabin lokaci Juan Valera ya barkewa Getafe kwallon a ragar Madrid ana minti 54.

Saura minti 16 a kammala wasa, Abdelaziz Barrada ya sake zira kwallo ta biyu a ragar Madrid.

A daya bangaren kuma Lionel Messi ne ya taimakawa Barcelona doke Osasuna ci 2-1 bayan ya zira kwallaye biyu a raga.

Saura kiris Tito Vilanova, ya sha kashi a karon farko domin Osasuna ce ta fara zira kwallo a ragar Barcelona ana minti 17 da fara wasan.

Yanzu hankali zai koma ne ga wasan Super Cup tsakanin Real Madrid da Barcelona a Bernebeu a ranar Alhamis, amma a karawar farko Barcelona ce ta doke Real Madrid ci 3-2.

Ingila

Arsene Wenger na Arsenal yace zai yi kokarin nemo hanyar wanda zai maye gurbin Robin Van Persie bayan Arsenal ta buga wasa karo na biyu ba tare da zira kwallo a raga ba tun fara Premier.

Arsenal ta buga wasa tsakaninta da Stoke da kuma Sunderland amma an tashi wasan ba tare da zira kwallo a raga ba.

A bara Robin Van Persie ya zira wa Arsenal kwallaye 37 a raga amma yanzu Manchester ta kwace dan wasan bayan zubawa Arsenal kudi Fam Miliyan 24.

Wenger yace a filin wasa babu fahimtar juna tsakanin sabbin ‘Yan wasan shi Lukas Podolski, da Olivier Giroud da Santi Cazorla,

A Old Trafford dai Van Persie ya bude tarihin zuba kwallaye a raga inda ya taimakawa Manchester United doke Fulham ci 3-2.

Wasa tsakanin Liverpool kuma da Manchester City an tashi ne ci 2-2. Kuma a wasan ne Carlos Tevez ya zira kwallon shi ta 100 a raga a Premier bayan samun Sa’ar Zirawa City kwallo ta biyu a ragar Liverpool.

A ranar Assabar ne kuma Kungiyar Chelsea ta doke Newcastle United ci 2-0, Hazard da Torres ne zuka zirawa Chelsea kwallayenta a raga a Stamford Bridge.

Faransa

A Faransa kuma kungiyoyin da suka jagoranci Teburin French League a matsayin na 1 da 2, Montpellier and Paris Saint-Germain har yanzu suna neman hanyoyin da za su lashe wasansu na farko a bana, domin an bar kungiyoyi biyu a baya a teburin gasar.

Bayan buga wasanni uku, Marseille ce ke jagoranci Tebur da maki biyu tsakaninta da Lyon da Valenciennes, Bordeaux da Toulouse.

Italiya

A Seria A a Italiya, AC Milan ta sha kashi hannun Sampdoria ci 1-0 a filin wasa na San Siro, Inter Milan kuma ta lallasa Pescara ci 3-0.

Sampodoria da Pescara dukkaninsu a bana ne suka tsallako zuwa Seria A. A ranar Assabar ne kuma Juventus ta fara yakin neman kare kambunta inda ta doke Perma ci 2-0.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.