Bayern da Juventus sun lashe Super Cup, City ta lashe Community Shield - Wasanni - RFI

 

Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h30 GMT
  Labarai 05/07/2015 06:00 GMT
 • 07h00 - 07h30 GMT
  Labarai 05/07/2015 07:00 GMT
 • 16h00 - 17h00 GMT
  Labarai 04/07/2015 16:00 GMT
 • 20h00 - 20h30 GMT
  Labarai 04/07/2015 20:00 GMT

Labaran karshe

 • Dan kunar bakin wake ya kashe mutane 5 a Potiskum
 • Fafaroma Francis ya sauka Equado a ziyarar kwanuki takwas da zai fara yanki Latin Amurka
 • Sepp Blatter ya soke halartar wasar karshe na gasar cin kopi Duniya na mata
 • Firaministan Girka yayi kira zuwa yan kasar na gani sun yi zabi na gari
 • Akala mutane 11 ne suka mutu bayan rubtawar wani kamfani takalma a China
Rufewa

Wasanni

Seria A Premier League Kwallon Kafa Bundesliga

Bayern da Juventus sun lashe Super Cup, City ta lashe Community Shield

media Jagoran 'Yan wasan Manchester City Vincent Kompany ya daga karkuwar Ingila da suka lashe bayan lallasa Chelsea REUTERS/Nigel Roddis

Kungiyar Bayern Munich ta lashe kofin Jamus na Super Cup bayan doke Borussia Dortmund ci 2-1. A Italiya, kungiyar Juventus ce ta lashe Super Cup bayan samun sa’ar Napoli. A Ingila kuma Manchester City ce ta lashe Community Shield bayan lallasa Chelsea ci 3-1.

Gab da fara wasa ne Bayern Munich ta zira kwallaye biyu a raga ana minti 11 da fara wasa. Ana kusan kammala wasa ne dan wasan Borussia Dortmund Robert Lewandowski ya zira kwallo daya.

A Italia kuma kungiyar Juventus ce ta lashe Super Cup bayan samun sa’ar Napoli. An dai kammala wasan ne ana ci 2-2. Amma bayan shiga lokuttan da aka kara ne Juventus ta samu sa’ar lashe wasan sanadiyar kwallon da dan wasan Napoli ya zira a ragarsu.

A Ingila kuma Manchester City ce ta lashe Community Shield bayan lallasa Chelsea ci 3-1.
Hakan kuma ke nuna Roberto Mancini ya shirya tsab domin kare kambun Premier da City zata fara bugawa a karshen makon gobe.

Fernando Torres ne dai ya fara zira kwallo a ragar City kafin Alkalin wasa ya ba Ivanovic jan kati. City ta samu barke kwallon ne ta kafar Yaya Toure, daga nan kuma Tevez da Samir Nasri suka sake zira wasu kwallyen biyu a raga.

Wannan na zuwa ne kuma a dai dai lokacin da Manchester City ke kammala cinikin Jack Rodwell daga Everton, amma babu wani bayani game da kudin cinikin dan wasan.
 

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure