Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Roberto Carlos ya yi ritaya daga taka kwallo

Guus Hiddink Kocin kungiyar Anzhi Makhachkala ta Rasha yace Dan wasan Brazil Roberto Carlos ya yi ritaya daga buga wasa. Carlos ya fara taka leda ne a shekarar 1991 a Brazil kafin ya tsallaka zuwa Turai zuwa kungiyar Inter Milan a shekarar 1995.

Roberto Carlos
Roberto Carlos
Talla

A 1996 ne Carlos ya koma buga wa Real Madrid Wasa a Spain har zuwa shekarar 2007. Carlos ya yi wasa da kungiyar Fenerbahce a Turkiya da kuma Corinthians a Brazil, kafin ya koma Anzhi a Rasha.

Robato Carlos ya bugawa kasar shi Brazil wasanni 125, ya buga gasar cin kofin duniya sau 3, a shekarar 1998 da Brazil tasha kashi hannun Faransa da kuma nasarorin da Brazil ta samu a Japan da korea ta kudu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.