Isa ga babban shafi
Tennis

Maria Sharapova ta lashe kofin Roland Garros

A ranar Assabar ne a karon Farko Maria Sharapova ‘Yar kasar Rasha ta lashe kofin gasar Rolland Garros ta French Open da ake gudanarwa a kasar Faransa bayan ta doke Sara Errani ta Italiya.

Maria Sharapova a Lokacin da take sunbatar Kofin da ta lashe bayan ta doke Sara Errani
Maria Sharapova a Lokacin da take sunbatar Kofin da ta lashe bayan ta doke Sara Errani Reuters/Regis Duvignau
Talla

Sharapova dai yanzu ta shiga sahun mata 10 suka lashe Roland Garros bayan ta lashe kofin Wimbledon da Us Open da Australian Open.

Li Na ‘Yar kasar China ita ce ta lashe kofin a bara kuma tun a zagayen Quarter Final ne aka yi waje da ita.

Victoria Azarenka ce da daya a duniya a fagen Tennis a bangaren mata, kodayake a Rolland Garros tasha kashi hannun Dominika ‘Yar kasar Slovakia.

Sharapova ce dai ke bi mata a matsayi na biyu, kuma ana hasashen Maria Sharapova zata iya karbe matsayin na daya a duniya saboda nasarar da ta samu a Roland Garros.

A bangaren Maza ruwan sama da aka tabka a birnin Paris a jiya Lahadi ya kawo tsaikun kammala wasan karshe a fafatwar Novak Djokovic da Rafel Nadal, a yau Litinin ne ‘yan wasan biyu zasu ci gaba da wasan.

Amma a fafatwar da aka yi a jiya Reafel Nadal ne ke kan gaba
Rafeal Nadal dai yana neman lashe kofin gasar ne karo na bakwai idan ya doke Novak Djokovic a wasan karshe

Novak Djokovic dai shi ne na daya a duniya kuma Rafeal Nadal ne ke bi masa a matsayin na biyu.

Sai dai Djokovic bai taba samun galabar Nadal ba a Rolanda Garros amma ya lallasa Nadal sau uku a wasu wasannin karshe da suka fafata.

Djokovic ne dai ya yi waje da Roger Federer a wasan kusa da karshe, kuma ya rama kashin da ya sha ne hannun Ferderer a bara.

A Roland Garoos a bana Novak Djokovic yana fatar kasancewa mutum na farko wanda ya lashe kofin gasar sau hudu Wimbledon da Australian Open da Us Open da Roland Garros tun bayan dan wasan duniya na Tennis Rod Laver a shekarar 1969.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.