Isa ga babban shafi
Tennis

Frech Open: Sharapova zata kara da Errani a wasan karshe

‘Yar kasar Rasha Maria Sharapova zata fafata da Sara Errani ta Italia a wasan karshe a ranar Assabar, bayan Sharapova ta samu nasarar doke Petra Kvitova ‘Yar kasar Jamhuriyyar Czech a zagayen kusa da karshe, inda kuma Errani ta Italia ta doke ‘Yar kasar Australia Samantha Stosur.

Maria Sharapova 'Yar wasan Tennis ta kasar Rasha
Maria Sharapova 'Yar wasan Tennis ta kasar Rasha Reuters
Talla

Akwai dai yiyuwar Sharapova zata karbe mukamn jaruwamar Tennis ta duniya idan har ta lashe kofin Roland Garros a Gobe Assabar. Bayan ta lashe Wimbledon a shekarar 2004 da US Open a 2006 da Australian Open a shekarar 2008.

Idan kuma Errani ta lashe kofin ita ce mace ta biyu daga Italia da ta lashe kofin bayan Francesca shekaru biyu da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.