Brazil
Gwamnatin Brazil ta amince a sayar da Giya a filayen wasa
Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta amince da kokar halatta sayar da giya a filin wasa a lokacin gasar cin kofin Duniya da za’a gudanar a Brazil a shekarar 2014.
Wallafawa ranar:
Talla
A watan jiya ne dai majalisar dattijan Brazil suka amince da kudirin dokar bayan haramta sayar da giyar a filiyen wasa a shekarar 2003.
Akwai dai masu adawa da wannan matakin a Brazil wadanda suke ganin sayar da giyar kan iya haifar da rikici a filayen wasa ta la’akari da kiyayya da ke tsakanin wasu magoya bayan kasashe musamman Brazil da Argentina.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu