Isa ga babban shafi
Tennis

Andy Murray ya fice gasar French Open

Andy Murray na Birtaniya ya fice gasar gasar Roland Garros ta Frech Open da ake gudanarwa a Faransa, bayan ya sha kashi hannun David Ferer na Spain a zagayen Quarter Final. Wannan ne karo na farko da David Ferer ya samu nasar tsallakewa zuwa zagayen kusa da karshe a gasar Roland Garros.

Dan wasan Tennis Andy Murray na Birtaniya
Dan wasan Tennis Andy Murray na Birtaniya REUTERS/Toby Melville
Talla

A ranar Juma’a ne zai hadu da zakaran gasar Rafael Nadal a fafafatawar neman zuwa zagayen karshe.

Sau shida Rafael Nadal ke lashe kofin French Open.

Nadal dai ya lallasa Nicolas Almagro ne a zagayen Quarter final wanda ya ba shi damar tsallakewa zuwa zagayen kusa da karsahe.

Andy murray yace ya yaba da kwazon shi a wasannin da ya buga a Roland Garros bayan ya sha kashi hannun David Ferer.

Akwai dai fafatwar zagayen kusa da karshe tsakanin Roger Federer da Novak Djokovic a ranar Juma’a.

Kuma cikinsu duk wanda ya samu sa’a shi zai kara da Rafael Nadal ko David Ferer a wasan karshe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.