Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA ta yi amai ta lashe kan mukamin Isah Hayatu na CAF

Hukumar kula da kwallon kafa ta Duniya FIFA ta yi amai ta lashe a sanarwar da hukumar ta bayar na zaben Isah Hayatu a matsayin shugaban kwamitin gudanar da wasannin Olympic. Hukumar tace kuskure aka samu wajen yada sanarwar a shfainta na Intanet.A sanarwar da hukumar ta yada a shafinta na Intanet (www.fifa.com) hukumar tace nan bada jimawa bane zata sanar da wadanda jasu jagoranci kwamitin gudanar da wasannin.Yanzu haka kuma hukumar ta cire sunan Hayatu daga jerin sunayen wadanda ake tunanin zasu jagoranci Ofishin FIFA na Goal Bereau wanda ke bada tallafi don ci gaban kwallon kafa a kasashen duniya.An samar da Shirin ne na Goal a shekarar 1999, wanda aka warewa kudi dala Miliyan 200. Yanzu haka kuma shirin ya gudanar da ayyukan ci gaba 500 a sassan kasashen duniya. 

Issa Hayatou Shugaban hukumar CAF
Issa Hayatou Shugaban hukumar CAF RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.