Isa ga babban shafi
Korea ta kudu

An Fara Shirin Gasan Nakasassu Na Olympics 2018

A Kasar Korea ta kudu,  Hukumomin kasar sunce  zasu kashe kudin daya kai Dolan Amirka kusan Miliyan 18 domin tanadar da kayan wasanni, saboda shirin gasan wasannin Motsa jiki na Olympics, na nakasassu  a shekara ta 2018.Dazun nan ayarin mutun 14 na komitin shirya gasan suka fara rangadin kwanaki 4 domin ganin shirin da akayi.Birnin Pyongchang na Korea ta kudun sun nemi karban bakuncin gasan na 2010 amma kuma birnin Vancuber suka kwace.Sun  sake neman na shekara ta  2014 amma kuma garin Sochi na kasar Russia sukayi nasara.A yanzu dai Korea ta Kudun na fafatawa ne da Annecy na kasar  Faransa, da Munich na Germus.Ranar 16 ga watan 7 na wannan shekaran za'a fidda inda zaayi gasan. 

Taswirar kasar Korea ta kudu
Taswirar kasar Korea ta kudu rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.