Isa ga babban shafi
Africa

Eto'o ne Gwarzon dan wasan kwallon kafa na Africa bana

Dan wasan kasar Kamaru Samuel Eto’o kuma mai taka leda a club din Inter Milan ne aka zaba gwarzon dan wasan kwallon kafa na bana a Africa kuma ya lashe kyautar a karo na hudu kenan. Eto’o mai shekaru 29, ya sami nasarar lashe kyautar ne bayan da ya doke abokan takararsa Asamoah Gyan na kasar Ghana da kuma Didier Drogba na Cote d’Ivoire yayin zaben da masu horar da ‘yan wasan Africa suka gudanar a birnin Al-Qahira ma Masar. Eto’o shi ne dan Africa da ya lashe kyautar gwarzon dan wasa har sau uku a jere tun daga shekarar 2003.A kakar wasan bara, Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan wadda samuel Eto’o ke taka mata leda, ita ce zakara a nahiyar Turai da wasan Serea A na Italiya, kana  kuma zura kwallayen tsohon dan wasan Real Madrid da Barcelona da Real Mallorca sun yi tasiri matuka ga nasarar da Inter Milan ta samu.Sai dai kuma dan wasan wanda ya jagoranci kasarsa Kamaru a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Africa ta kudu, inda ba su taka wata rawar a zo a gani ba, hasali ma  Kamaru ce kasa ta farko da aka fara korawa gida daga Africa ta kudu. Tun da an ce waiwaye adon tafiya, ga jerin sunayen gwarzayen ‘yan wasan kwallon kafa a nahiyar Africa wadanda suka gabata. 1970 - Salif Keita (MLI)1971 - Ibrahim Sunday (GHA)1972 - Cherif Souleymane (GUI)1973 - Tshimen Bwanga (COD)1974 - Paul Moukila (CGO)1975 - Ahmed Faras (MAR)1976 - Roger Milla (CMR)1977 - Tarak Dhiab (TUN)1978 - Abdul Razak (GHA)1979 - Thomas Nkono (CMR)1980 - Jean-Manga Onguene (CMR)1981 - Lakhdar Belloumi (ALG)1982 - Thomas Nkono (CMR)1983 - Mahmoud al-Khatib (EGY)1984 - Theophile Abega (CMR)1985 - Mohamed Timoumi (MAR)1986 - Badou Zaki (MAR)1987 - Rabah Madjer (ALG)1988 - Kalusha Bwalya (ZAM)1989 - George Weah (LBR)1990 - Roger Milla (CMR)1991 - Abedi 'Pele' Ayew (GHA)1992 - Abedi 'Pele' Ayew (GHA)1993 - Abedi 'Pele' Ayew (GHA)1994 - George Weah (LBR) and Emmanuel Amunike (NGR)1995 - George Weah (LBR)1996 - Nwankwo Kanu (NGR)1997 - Victor Ikpeba (NGR)1998 - Mustapha Hadji (MAR)1999 - Nwankwo Kanu (NGR)2000 - Patrick Mboma (CMR)2001 - El-Hadji Diouf (SEN)2002 - El-Hadji Diouf (SEN)2003 - Samuel Eto'o (CMR)2004 - Samuel Eto'o (CMR)2005 - Samuel Eto'o (CMR)2006 - Didier Drogba (CIV)2007 - Frederic Kanoute (MLI)2008 - Emmanuel Adebayor (TOG)2009 - Didier Drogba (CIV)2010 - Samuel Eto'o (CMR)Akwai kuma sauran kyautuka da dama da aka bayar ga sauran wadanda suka nuna bajinta a fagen wasan na kwallon kafa a Africa da suka hadar da; Ahmed Hassan mai taka leda a club din Al Ahly da ya lashe kyautar dan wasan da yafi nuna kwazo a wasannin cikin gida na Africa.Kwadwo Asamoah dake taka leda a club din Udinese na kasar Italiya ya lashe kyautar matashin dan wasa mai kazar-kazar a Africa. Ghana ce ta lashe kyautar kasar da ta fi nuna bajinta a tsakanin kasashen Africa.TP Mazembe na jamhuriyyar Demokradiyyar Congo kuma ya zamo kulob din da ya fi taka rawar gani a Africa. Mai horas da 'ya wasan kasar Ghana Milovan Rajevac shi ya lashe kyautar Kociyan-kociyoyi na Africa. A mata kuma Perpetua Nkwocha "yar Najeriya ce aka bai wa kyautar gwanar 'yar wasan kwallon kafa a Africa. Nigeriya ce ta lashe kyautar fitacciyar kungiyar wasan kwallon kafa ta mata a Africa. 

Dan wasan da ya fi gwaninta a  fagen kwallon kafan Africa a 2010 Samuel Eto'o dan kasar Camaru
Dan wasan da ya fi gwaninta a fagen kwallon kafan Africa a 2010 Samuel Eto'o dan kasar Camaru Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.