Isa ga babban shafi
Birtaniya

'Yan siyasan Birtaniya na rufa - rufa a binciken cin zarafi - rahoto

Wani bincike da aka gudanar a Birtaniya ya nuna yadda gwamnati, majalisar dokoki da jam’iyyun siyasa suka nuna halin ko – in- kula ga batun cin zarafin yara, inda har wani lokaci ma suke kare masu aikata haka ta wajen yin rufa – rufa.

Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth II tare da Yarima Philip a majalisar dokokin kasar./
Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth II tare da Yarima Philip a majalisar dokokin kasar./ Reuters
Talla

Rahoton kwamitin binciken ya gano yadda hukumomi a Westminster suka yi wa batutuwan da suka shafi zarge zargen cin zarafi rikon sakainar kashi musammamn ma ‘yan sanda, masu gabatar da kara da sauransu.

Dalilin wannan rahoton ne ma wani tsohon shugaban jam’iyyar masu sassaucin ra’ayi na Liberal party ya sanar da yin murabus daga majalisar dattawa, bayan rahoton ya caccaki gazawarsa wajen daukar mataki a kan wani dan majalisa mai cin zarafin yara.

Sai dai rahoton na kwamitin kan cin zarafin yara bai gano wata shaida mai karfi kan wanzuwar wani gungu da ya kunshi manyan ‘yan siyasa masu aikata laifin ba.

A cikin shekarun 1960, 1970 da 1980s, akwai ‘yan majalisar dokoki kamar su Cyril Smith dan jam’iyyar Liberal, da Peter Morrison na Conservative, wadanda suka yi kaurin suna wajen bayyana sha’awarsu ga neman yara masu karancin shekaru, amma kuma ba kunya ba tsoro aka kare su daga fuskantar kulliya.

Ko a shekarar 2017, sai da wata ‘yar takara ta jam’iyyar Green party ta nada mahaifinta a matsayin wakilin jam’iyya a zabe duk da cewa kotu ta taba daureshi kan laifin yi wa wani yaro fyade.

A shekarar 2015 aka kafa wannan kwamitin binciken biyo bayan manyan jerin dambarwar cin zarafi, ciki harda na wani tsohon mai gabtar da shirye shiryen talabin na BBC marigayi Jimmy Savile.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.