Isa ga babban shafi

Coronavirus ta yi mummunar yaduwa cikin sa'o'i 24

Cutar Murar Mashako ta Coronavirus ko COVID-19 na saurin yaduwa a wasu kasashen duniya nesa da China inda ta samo asali, bayan da wasu kasashe suka sanar da bayyanar cutar a karon farko Litinin din nan, ya yin da Cutar ta hallaka mutane kimanin 150 a mahaifarta wato China.Ga dai yadda cutar ta bazu cikin awa 24 a duniya, wato ranar Litinin kadai.

Cutar coronavirus na yaduwa kasashen duniya
Cutar coronavirus na yaduwa kasashen duniya REUTERS/Manuel Silvestri
Talla

Daga ranar Litinin adadin wadanda Annobar cutar murar Mashako ta Coronavirus ta hallaka a China ya kai dubu 2,592, bayan da mahukuntan Bejin suka sanar da karin mutuwar mutane 150 a rana guda, ya yin da kasar ta samu karin sabbin wadanda suka kamu da cutar har 409, abin da ya kara adadin zuwa sama da mutane dubu 77.

Shugaba Xi Jinping ya bayyana cutar a matsayin babbar kalubale da kasar ta fuskanta a bangaren kiwon lafiya tun daga shekarar 1949, tare da dage zaman Majalisar dokokin kasar, zuwa ranar 5 ga watan Maris, mataki irin sa na farko cikin shekaru 30,ya yin da ta kuma dauki matakin haramcin nan take kan kasuwancin namun daji da amfani dasu.

Korea ta Kudu ta kasance kasa ta biyu da Cutar Covid-19 tafi addaba bayan China, sakamon karin sabbin mutane 161,abin da ya haurar da addadin wadanda ke fama da annobar zuwa 763, inda tuni ta hallaka mutane 7, shugaba Moon Jae-In ya sanarda yanayin dokar ta baci dangane da cutar.

A yankin Gabas ta Tsakiya, Kasar Iran ke ja gaba danagne da Cutar Coronavirus, inda mutane 12 suka mutu cikin 64 da suka kamu da cutar. Kimanin mutane 250 aka killace a Kasashen Armeniya da Turkiya da Jordan da kuma Pakistan, ya yin da kasar Afghanistan ta rufe iyakanta da kasashen.

Italiya ce kasar da Cutar tafi kamari a Nahiyar Turai, inda tuni mutane 6 suka mutu a kasar cikin 219 da suka kamu da cutar, tuni kasar ta sanar da killace wasu biranai 11 na arawacin kasar har na tsawon makonni biyu.

A halin da ake ciki kasashen Iraki da Koweit da Bahrein da kuma Oman duk sun sanarda bayyana cutar a kasashen su a Litinin din nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.