Putin dan jagaliya ne, mai murkushe dimokaradiya - Sanders
Dan takaran shugaban kasar Amurka karkashin inuwar jam’iyyar Democrat, Bernie Sanders ya gargadi Rasha da kada tayi katsalandan a zaben kasar mai zuwa biyo bayan rahotannin da ke nuni da cewa kasar tana neman tsoma baki a zaben Amurka, duk da cewa ba a gama cece kuce kan zargin aikata haka da ake mata a zaben 2016 ba.
Wallafawa ranar:
Sanders ya shaida wa manema labarai cewa hukumomin kasar sun tsegunta mai take taken Rasha na yi musu katsalandan a zaben 2020 kusan wata guda da ya wuce.
Sanders ya ce bai dauki shugaban Rasha Vladimir Putin a matsayin babban aboki kamar yadda shugaba Donald Trump ya dauke shi ba, yana mai bayyana shi a matsayin mai kama karya, kuma dan jagaliya da ke kokarin murkushe dimokaradiya a Rasha.
Wadannan kalamai na sanders na zuwa ne jim kadan bayan jaridar ‘The Washington Post’ ta ruwaito cewa wasu bayanan sirri na nuni da cewa Rasha na neman taimaka masa a yakin neman zabe.
Sai dai ba a bayyana irin taimakon da Rasha ke son yi ba, amma Sanders na ganin ba zai rasa nasaba da wasu zafafan kalaman da wasu suka wallafa a intanet ba da ya janyo suka daga takwarorinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu