Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus ta zurfafa bincike kan harin Hanau

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi Allah-wadai da mummunan harin bindiga da wani mai tsattsauran ra’ayin wariyar launin fata ya kai shagon shan shayi da tabar-shisha a garin Hanau, inda ya kashe mutane 9 nan take.

Hukumomin Jamus na bincike don gano masu hannu a harin Hanau da ya kashe mutane 9
Hukumomin Jamus na bincike don gano masu hannu a harin Hanau da ya kashe mutane 9 REUTERS/Kai Pfaffenbach
Talla

Dan bindigar mai suna Tobias R. mai shekaru 43, an same shi a mace a gidansa bayan jami'an tsaro sun dukufa wajen neman sa ruwa a jallo.

Baya ga gawar tasa, an kuma samu gawar mahaifiyarsa mai shekaru 72 a cikin gidan nasa.

A cewar gwanayen binciken kwakwaf na Jamus,  akwai alamun mutumin mai kyamar baki ne sosai.

Shugabar Gwamnatin Jamus ta ce, nuna kyama ko launin fata mummunar guba ce da ke tattare da wasu Jamusawa.

Bayanai na cewa, mutumin ya bar sakon manufofinsa da wasu hotunan bidiyo da ke nuna harin ta'addanci ne ya kai kan baki ‘yan kasashen waje.

Akasarin mamatan da harin ya rutsa da su, Kurdawa ne da ke zaune a  Jamus.

Yanzu haka masu bincike sun mayara da hankali don gano ko wasu mutane na da hannu ko kuma masaniya game da wannan harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.