Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai-Amurka

Lokaci yayi da zamu daina dogaro da Amurka - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci kasashen yammacin Turai da su karfafa rundunonin tsaronsu ciki har da mallakar nukiliya da kuma samun fasahohin kariya daga makaman kare dangin.

Shugaban Faransa  Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Macron ya bayyana haka ne yayin taron kasashe kan sha’anin tsaro a duniya, da yau ake kammala shi a birnin Munich na Jamus.

Shugaban na Faransa ya kuma ce lokaci yayi dakasashen Yammacin Turai za su daina dogaro da Amurka musamman ta fuskar tsaro, kamar yadda lamarin yake tun bayan kammala yakin duniya na 2.

Shi kuwa sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da ya halarci taron na kasadakasa kan tsaro a duniya, nanata cewa yayi, gwamnatin shugaba Donald Trump bata kokarin janyewa daga jagorancin duniya kamar yadda kasashen na Yammacin Turai ke zargi, sai ma kokarin hada kansu da take yi.

Pompeo ya ce babbar matsalar da Amurka ke fuskanta, ita ce mafi akasarin kawayenta na dari-darin goya mata baya a rikicin da take yi da kasar Iran, da kuma kin cika alkawuran baiwa rundunar kawancen tsaro ta NATO gudunmawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.