Isa ga babban shafi

Annobar COVID-19 ta kashe mutum na farko a wajen Asia

Hukumomin Kasar Faransa sun sanar da mutuwar mutumin farko da ya kamu da cutar coronavirus ko COVID-19 a wajen nahiyar Asia, sakamakon mutuwar wani dattijo mai shekaru 80 dake ziyara a Paris.

Yadda kasashe ke daukar matakan hana yaduwar cutar Coranavirus
Yadda kasashe ke daukar matakan hana yaduwar cutar Coranavirus REUTERS/Kham
Talla

Minister lafiyar kasar Agnes Buzyn tace an sanar da ita mutuwar mutumin wanda yake kwance a asibitin Paris tun daga watan jiya, bayan tabarbarewar lafiyar sa.

Wannan shi ya kawo adadin mutanen 4 da suka mutu sakamakon wannan annoba a wajen kasar China, bayan wadanda suka mutu a kasashen Philippines da Hong Kong da kuma Japan.

Ita dai wannan annoba tayi kamari a cikin wannan mako a Yankin Hubei dake China, inda aka tabbatar da mutuwar mutane 143 abinda ya kawo adadin mutanen da suka mutu baki daya zuwa 1,523.

Kasashe da dama sun haramtawa bakin dake zuwa daga China shiga kasar su, yayin da ita ma Chinar ta hana Yan kasar ta tafiye tafiye.

Ko a jiya sanda aka tabbatar da samun cutar a Masar, wanda shine irin sa na farko a nahiyar firka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.