Isa ga babban shafi
Turkiya

Zaftarowar tsaunin kankara ya hallaka kusan mutum 40 a Turkiya

Mahukuntan Turkiya sun tabbatar da mutuwar mutane 38 baya ga jikkatar wasu da dama sakamakon iftila’in zaftarowar kankarar da yankin gabashin kasar ya fuskanta daga yammacin jiya Talata zuwa yau Laraba.

Zaftarowar tsaunukan kankara a yankin Van na gabashin Turkiya.
Zaftarowar tsaunukan kankara a yankin Van na gabashin Turkiya. Mandatory credit Kyodo/via REUTERS
Talla

Kamfanin dillancin labaran Turkiya Anadolu da ke tabbatar da mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar zaftarowar tsaunukan kankarar a yau Laraba, ya bayyana yadda aka gano gawarwakin jami’an agaji 14 da kuma wasu fararen hula 19 wadanda kankarar ta rufe tun a yammacin jiya Talata.

Ka zalika majiyar labarai ta ruwaito gwamnan yankin Van a gabashin kasar ta Turkiya Mehmet Emin Bilmez na cewa an gano wata motar safa dauke da mutane 5 da itama kankarar ta bunne tare da hallaka ilahirin fasinjan cikin, adadin da ya mayar da mutanen da zaftarowar kankarar ta kashe zuwa mutum 38.

A cewar gwamnan na Van jami’an agaji na ci gaba da kai dauki don lalubo wadanda suka nutse cikin dusar kankarar duk kuwa da yadda zaftarowar kankarar ya haddasa matsalar sufuri musamman bayan da rufe manyan titunan yankin.

Kafafen talabijin a kasar ta Turkiya sun rika haska yadda kankarar ta lullube gidaje da manyan hanyoyi baya ga bannar da ta ke ci gaba da yiwa yankin.

Ministan lafiya Fahrettin Koca ya ce yanzu haka akwai mutane 53 da aka yi nasarar cetowa da ransu kuma suna karbar kulawar gaggawa a asibiti ko da dai ya ce adadin ka iya karuwa dai dai lokacin da jami’an agaji na hukumar AFAD ke ci gaba da kai dauki yankin na Van.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.