Isa ga babban shafi
Faransa

Tayin gwamnati ya gaza dakatar da yajin aiki a Faransa

Yajin aikin sufuri mafi tsawo a tarihin Faransa da kuma zanga-zangar adawa da sabuwar dokar fansho sun shiga rana ta 39, duk da tayin yiwa dokar kwaskwarima da gwamnati tayi.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Faransa.
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Faransa. REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Sashin dokar fanshon da ya fusata kungiyoyin kwadagon Faransa dai shi ne karin shekarun ritaya daga 62 zuwa 64 da kuma banbanta adadin kudaden da za a biya wadanda suka zabi ajiye aiki a shekarun.

A baya bayan nan ne kuma Fira Minista Edouard Philippe ya bayyana shirin janye kudirin kara shekarun na ritaya, sai dai tayin ba yi tasirin kawo karshen yajin aikin da ya kassara fannonin sufurin jiragen kasa na cikin gari da tsakanin gari da gari, da motocin Safa ba.

Ma’aikatar harkokin cikin gidan Faransa ta ce akalla masu zanga-zanagr adawada sabuwar dokar fanshon dubu 149 ne suka fito a ranar asabar 11 ga Janairun 2020.

Baya ga karin shekarun ritaya, daya daga cikin sauye-sauyen da shugaba Emmanuel Macron ke son yi shi ne hade kamfanonin lura da hakkokin ‘yan fansho 42 zuwa kamfani 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.