Isa ga babban shafi
Turai

Majalisar Britania ta amince da ficewa daga kungiyar Turai

Wakilan Majalisar Britania sun zartas da amincewa da ficewa daga cikin kungiyar Tarayar Turai karshen wannan wata , al’amarin da zai kawo karshen jayayyar da aka kwashe lokaci mai tsawo ana yi da kuma ya so raba kawunan ‘yan kasar.

Borris Johnson Firaministan Birtaniya
Borris Johnson Firaministan Birtaniya REUTERS/Peter Nicholls
Talla

Da tafi da murna ne dai wakilan majalisar suka zartas da batun ficewar da rinjaye mai yawa wato kuri’u 330 bisa kuri’u 231.

Tun fara batun ficewar Britania daga cikin kungiyar Tarayar Turai a shekara ta 2016, yasu-yasu wakilan majalisar dokokin na Turai sun sha kai ruwa rana wasu na ganin babu wani dalili da zai sa su rabu da kasashen dake makwabtaka dasu a kungiyarce na tsawon shekaru 50.

Kamfanoni da dama da Gwamnatoci a Turai na fargaban makomar su idan har Britania ta fice daga cikin kungiyar ta su.

Kafofin yada labarai da yawa dai basu bada wani muhimmanci ba bayan amincewar wakilan majalisar a jiya na baiwa Firaminista Boris Johnson izinin salube kasar daga cikin kungiyat Tarayar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.