Isa ga babban shafi
Faransa

Gwamnatin Faransa na son cimma matsaya da 'yan kwadago

Gwamnatin Faransa da kungiyoyin kwadago za su koma teburin tattaunawa a wannan Talata da zummar lalubo hanyar warware sabaninsu kan kudirin dokar fansho wanda ya haddasa yajin aiki mafi tsawo a cikin gomman shekaru a kasar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Christophe ARCHAMBAULT / AFP
Talla

Firaministan Faransa, Edouard Philippe ya ce, kofarsu a bude take domin gudanar da tattaunawa a daidai lokacin da tankiyar da ke tsakanin gwamnati da’yan kwadago ta tsananta, inda aka girke jami’an ‘yan sanda a wasu matatun man fetir domin hana masu zanga-zanga dakile hanyoyi.

Firaminsta Philippe ya ce, akwai bukatar kowanne bangare ya sassauta matsayarsa a yayin da aka shiga kwana ta 34 da gudanar da yajin aikin da ya haddasa tarnaki a bangaren sufurin kasar.

Kodayake Firaminsitan ya nanata cewa, gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ba za ta yi watsi da shirinta na samar da sauye-sauye a dokar kudaden fanshon ba, wanda ya bukaci jinkirta ritayar ma’aikata.

Daga cikin kungiyoyin kwadagon akwai CFDT mai sassaucin ra’ayi wadda gwamnatin Faransa ke fatan cimma yarjejeniya da ita domin kawo karshen yajin aikin.

To sai dai CFDT ta bayyana shakku kan bukatun da gwamnatin ta gabatar mata na tsawaita shekarun ritayar ma’aikata zuwa shekara 64.

Kungiyar ta CFDT ta bakin shugabanta, Laurent Berger ce, dole ne gwamnatin ta janye wannan batu na tsawita shekarun ritayar.

A martanin da ya mayar, Firamiista Philippe ya ce, muddin kungiyoyin kwadagon za su gabatar masa da gamsasshiyar hanyar rage gibin kudin fanshon, to babu shakka zai amince da haka.

Ita kuwa CGT wadda ta fi ra’ayin rikau daga cikin kungiyoyin kwadagon cewa ta yi, dole ne gwamnatin ta soke shirin sauye-sauyen dokar fanshon baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.