Isa ga babban shafi
Faransa

Gwamnatin Faransa ba za ta jingine shirin fansho ba

Fadar gwamnatin Faransa ta ce, shugaba Emmanuel Macron ba zai soke sabon shirin biyan kudaden fanshon da ya haddasa yajin aikin gama-gari da kuma jerin zanga-zanga a fadin kasar ba.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ludovic MARIN / AFP
Talla

Gwamnatin Macron ta ce, abin da za ta yi a halin yanzu shi ne, inganta shirin na biyan fansho, amma ba soke shi baki daya ba.

Wani jami’in gwamnatin kasar da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, akwai yiwuwar a sauya bangaren shakaru 64 na ritayar kamar yadda sabon shirin ya kunsa, inda ma’aikaci zai cancaci karbar cikakken fansho sabanin kudirin farko na sabon shirin.

Dama ma dai, wannan bangaren ne ya fi harzuka kungiyoyin kwadagon kasar har suka gudanar da yajin aikin makwanni biyu da ya gurgunta harkokin sufuri.

Shugaba Macron na fatan zaman tattaunawar da za a yi tsakaninsa da shugabannin ‘yan kwadagon zai yi sanadin jingine yajin akin domin bai wa al’umma damar tafiye-tafiye kamar yadda suka shirya a daidai wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara.

Akallla mutane dubu 615 ne suka shiga tarukan gangamin da aka gudanar a ranar  Talata a sassan Faransa domin nuna adawa da shirin na fansho, yayin da jami’an ‘yan sanda suka cilla borkonon-tsohuwa kan masu zanga-zangar a birnin Paris tare da kame 30 daga cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.