Isa ga babban shafi
Turai

Za a kayyadewa masana'antun Turai adadin hayakin da suke fitarwa

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai sun cimma matsayar bayar da kariya ga masana’antunsu ta yadda za su kayyade adadin hayaki mai gurbata muhalli da kowacce ma’aikata za ta rika fitarwa baya ga sanya haraji kan duk wata masana’anta ko kasar da ta ketare iyaka kan adadin da aka kayyade.

Tiriri da gurbataccen hayaki mai haddasa dumamar yanayi da masana'antu ke fitarwa.
Tiriri da gurbataccen hayaki mai haddasa dumamar yanayi da masana'antu ke fitarwa. Reuters/Stringer
Talla

Shugabannin na Turai wadanda suka cimma wannan matsaya yau juma’a yayin taronsu da ya gudana can a birnin Brussels na Belgium, sun ce ta haka ne za su kai ga nasara kan kudirinsu na yakar dumamar yanayi ta hanyar rage hayaki mai gurbata muhalli.

Faransa wadda ke matsayin ja gaba a shirin yaki da dumamar yanayi a duniya, ta ce kowacce kasa za ta sana dadin hayakin da ma’aikatanta ya kamata su rika fitarwa.

A cewar Faransar ta hanyar bin wannan tsari ne, za’a samu nasarar cimma kudirin yakar dumamar yanayi nan da shekarar 2050 yayinda za a ci tarar duk wata masana’antar ketare da ke nahiyar ta Turai matukar ta ki mutunta adadin da aka kayyade mata na yawan hayakin mai gurbata muhallai da ta ke fitarwa.

Matakin shugaban na Tarayyar Turai na zuwa a daidai lokacin da masana ke kara jan hankalin shugabanni kan illar da tuni dumamar yanayi ta fara yiwa halittun ban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.