Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 17/01 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 12/01 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/01 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 17/01 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/01 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 17/01 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/01 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 17/01 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/01 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 17/01 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/01 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/01 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 17/01 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/01 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 17/01 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 17/01 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/01 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/01 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 17/01 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Turai

Macron na jagorantar taron sasanta rikicin Ukraine

media Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin. Gerard Julien/Pool via REUTERS

Yau ne shugaban Faransa Emmanuel Macron ke karbar bakoncin taron neman kawo karshen rikicin gabashin Ukraine da ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 13 tun daga shekarar 2014. Ana kallon wannan taron a matsayin zakaran-gwajin- dafi ga tasirin Macron a huldarsa ta kai tsaye da Rasha.

Shugaba Macron tare da hadin gwiwar shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, zai hada shugaban Rasha Vladmir Putin da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky a wuri guda domin tattaunawar keke da keke wadda ita ce irinta ta farko a tsakaninsu.

Tuni jami’an diflomasiya suka yi gargadi danagane da sakamakon wannan zama, inda suke ganin cewa gazawa cimma matsaya, za ta yi nakasu ga tasirin Macron wanda ya shirya taron duk da zanga-zangar da ta gurgunta harkokin sufuri a Faransa.

Michel Duclos, tsohon jami’in diflomasiya kuma mamba a Cibiyar nazarin kwararru ta Montaigne da ke Faransa, ya ce, wannan taro na a matsayin zakaran gwajin dafi ga shugaba Macron da sauran Turawa, yana mai cewa, muddin shugaban ya gaza samun kayyakawan sakamako a kan Ukraine, babu shakka za a ci gaba da ware shi.

Mista Duclos na ganin cewa, shugaba Putin na Rasha zai halarci taron ne domin amfani da wata dama ta sake rarraba kawun kasashen Turai.

Macron dai na ci gaba da kokarin nuna kansa a fagen siyasar duniya a ‘yan watanni nan a daidai lokacin da kasar Jamus ta dan ja baya a harkar diflomasiya saboda shirye-shiryen uwargida Merkel na barin gado.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure