Isa ga babban shafi
Faransa-Sahel

Macron ya nuna bacin rai kan kyamar da akewa Sojin Faransa a Sahel

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya ce idan har kasashe 5 na yankin Sahel na bukatar ci gaba da kasancewar dakarunsa a cikin kasashensu, to ya zama wajibi su gabatar da bukatar hakan a rubuce.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Bertrand Guay/Pool via REUTERS
Talla

Macron, wanda ke zantawa da manema labarai a gefen taron kungiyar tsaro ta NATO yau laraba a birnin London, ya ce dakarunsa ba za su ci gaba da kasancewa a wadannan kasashen ba a daidai lokacin da ake nuna masu kyama.

Cikin kalaman shugaban na Faransa ya bayyana cewa babu wata tantama a game da halascin kasancewar dakarun kasar da kuma fadan da su ke gwabzawa a yankin Sahel, face matakan da suke dauka don tabbatar da tsaro baki daya, adon haka kasancewarmu a can ba wani abu ba ne.

Macron ya ci gaba da cewa ''A yau ba wani yanki a duniya da ke fama da irin kalubalen da Sahel ke fama da su, da suka hada da ta’addanci, sauyin yanayi, yawan haihuwa da kuma fasakori, doli mu taunkari wadannan matsaloli amma ba mu kadai ba''.

''Abu na biyu kuwa, ya zama wajibi mun fayyace a hukumance halascin kasancewar dakarunmu a yankin Sahel, saboda haka ina sauraren kasashe biyar na yankin Sahel su gabatar wa Faransa da sauran kasashen duniya bukatunsu a hukumance, shin wai suna bukatar mu a kasashensu ko a’a, ina son sun ba mu amsa dangane da haka''.

Emmanuel Macron ya karkare da cewa ''Ni dai ba na bukatar kasancewar sojin Faransa a wata kasa ta Sahel a dai dai lokacin da ake nuna wa Faransa kyama, kuma a cikin masu nuna wannan kyamar har da manyan ‘yan siyasa''.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.