Isa ga babban shafi
Turai

An kama wasu jami'an Andalusia a Spain

Wata Kotu a Spain ta samu wasu manyan jami’an tsohuwar gwamnatin Andalusia guda 19 da laifin cin hanci da rashawa mafi girma da aka taba gani a tarihin kasar.

Wasu daga cikin yan kasar Spain a lokacin zaben kasar
Wasu daga cikin yan kasar Spain a lokacin zaben kasar REUTERS/Susana Vera
Talla

Kotun ta samu mutanen ne da takardar euro miliyan 680 da aka ware domin marasa ayyukan yi da kuma kamfanonin dake fama da matsala.

Hukuncin kotu na zuwa ne a daidai lokacin da Firaminista Pedro Sanchez ke godon samun goyan bayan kafa sabuwar gwamnati.

A dan tsakanin nan ne aka gudanar da zaben kasar , Al’uammar kasar Spain sun kada kuri’a a babban zabe na hudu cikin shekaru da dama, yayin da ake ci gaba da zaman dar – dar sakamakon gwagwarmayar ‘yan awaren Catalonia.

Sake gudanar da wannan zabe dai ya biyo bayan gaza samun goyon baya da Firaminista Pedro Sanchez ya yi ne daga sauran jam’iyyun siyasa, biyo bayan zaben watan Afrilu da bai kammalu ba, inda jam’iyyarsa ta Socialist party ta samu mafi rinjayen kuri’u, amma ta samu akasin haka a majalisar dokoki.

Sai dai bisa dukkan alamu dai kwalliya ba za ta biya kudin sabulu ba a zaben baya –bayan nan. Babu jami’iyyar da ake ganin za ta fi rinjaye a majalisar dokokin Spain mai kujeru 350 daga cikin jam’iyyun da ke takara a zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.