Isa ga babban shafi

Macron zai shiga tsakanin Putin da Zelensky

Kasar Faransa zata karbi bakuncin wani taron kasashe 4 da zai gudana a Paris kan yadda za’a warware rikicin Ukraine ranar 9 ga watan Disamba mai zuwa, wanda zai samu halartar shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaran sa na Ukraine Volodymyr Zelensky da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Shugaban Faransa  Emmanuel Macron da takwaran aikinsa na Rasha Vladimir Putin
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaran aikinsa na Rasha Vladimir Putin REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Fadar shugaban Faransa tace shugaba Emmanuel Macron na fatar ganin taron ya warware duk wata sarkakiyar da ta rage na rikicin, bayan nasarorin da ake cigaba da samu tsakanin Rasha da Ukraine.

Faransa tace tana fatar ganin wannan taron ya bada damar bude wani sabon babi wajen aiwatar da yarjeniyoyin da aka amince da su a shekarar 2014 da 2015 amma aka gaza amfani da su.

Dakarun Ukraine da mayakan yan awaren dake samun goyan bayan Moscow sun kammala janyewa daga inda suka ja daga ranar Asabar da ta gabata, wanda ke cikin sharuddan gudanar da wannan taro.

Wannan dai yunkuri ne da Faransa ke jagoranci na magance rikicin da ya lakume rayukan mutane sama da 13,000, lokacin da Rasha ta mamaye wani yanki na Ukraine a shekarar 2014 dake tsibirin Crimea, matakin da ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin ta da kasashen Yammacin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.