Isa ga babban shafi
Turkiya-Turai

Erdoga na barazanar bude wa 'yan ci-rani kofar shiga Turai

Shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan, ya sake yin barazanar bude iyakokin kasar domin bai wa ‘yan ci-rani damar tsallakawa zuwa Turai, matukar dai kasashen duniya suka ki bai wa Turkiyya karin tallafi don hana kwararar bakin.

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan REUTERS/Huseyin Aldemir
Talla

Shugaba Erdogan wanda ke gabatar da taron manema labaran hadin-gwiwa da Firaministan Hungry mai tsatsauran ra’ayin Viktor Orban, ya ce ko da tallafi ko babu, Turkiyya za ta ci gaba da kula da dubban ‘yan ci-rani da ke kasar, amma za a iya kai wa lokacin da kasar za ta bude iyakokinnta don bakin su fice a cewarsa.

Erdogan ya ce wannan tunatarwa ce kamar yadda ya taba yi wa kasashen duniya kashedi a baya, yana mai cewa idan aka bude iyakokin kasar, daga nan ‘yan ci-ranin sun san inda za su dosa.

Shugaban na Turkiyya ya yi kira ga kasashen Turai su bai wa kasar tallafin kudade domin aiwatar da shirinsa na samar da yankin tudun mun tsira kusa da iyakar kasar da Syria, saboda a can ne ake da dubban ‘yan gudun hijira a cewarsa.

Firaministan Hungry Viktor Orban, na daga cikin shugabannin da ke matukar kyamar ‘yan gudun hijira da ma ‘yan ci-rani musamman wadanda suka fito daga kasashen musulmi, kuma sau da dama yana nuna goyon baya ga Erdogan, wanda ke cewa kamata ya yi a mayar da bakin zuwa kasashensu na asali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.