Isa ga babban shafi
Faransa

'Yan sanda sun tasa keyar 'yan ci-rani a birnin Paris

Jami’an ‘yan sandan Faransa sun kwashe sama da ‘yan gudun hijira 1,600 daga wasu sansanoninsu guda biyu da ke yankin arewacin birnin Paris a wannan Alhamis. Matakin na zuwa ne kwana guda da gwamnatin kasar ta kaddamar da sabbbin tsauraran matakan kula da sha’anin shige da fice a kasar.

A yayin gudanar da aikin kwashe 'yan cirani daga sansanoninsu da ke arewacin birnin Paris na Faransa
A yayin gudanar da aikin kwashe 'yan cirani daga sansanoninsu da ke arewacin birnin Paris na Faransa MARTIN BUREAU / AFP
Talla

Kimanin jami’an ‘yan sandan Faransa 600 ne suka tasa keyar ‘yan ci-ranin daga rumfunan da suke samun mafaka zuwa wasu cibiyoyi na daban, kuma an gudanar da wannan gagarumin aikin ne a daidai lokacin da ruwan sama ke sauka.

Da dama daga cikin wadannan ‘ yan ci-rani sun fito ne daga Afghanistan da kuma kasashen Afrika da ke yankin Kudu da Sahara.

A yayin zantawa da mane labarai, shugaban ‘yan sandan birnin Paris, Didier Lallement ya ce, ba za su lamunci yanayi mai cike da hatsari irin wannan ba.

Lallement ya ce, wannan aikin da suka gudanar, wani bangare ne na aiwatar da shirin gwamnatin kasar dangane da shige da fice.

Gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta lashi takobin tunkarar duk wata matsalar da ta jibanci sha’anin shige da fice a kasar, amma ana kallon wannan shiri nata a matsayin yunkurin hana jam’iyyun masu tsattsauran ra’ayi sayen kuri’un jama’a a zaben kananan hukumomi da zai gudana a badi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.