Isa ga babban shafi

EU tace kofarta a bude take domin tattaunawar fahimta juna da Birtaniya kan Brexit

Kungiyar Tarayyar Turai ta nuna rahin gamsuwarta da sabbin kudurorin ficewar Birtaniya daga gungun kasashen, amma ta ce, kofarta a bude take domin zaman tattaunawar fahimtar juna da Birtaniyar.

Tutotin Turai da na Birtaniya, wato alamar Brexit
Tutotin Turai da na Birtaniya, wato alamar Brexit REUTERS/Peter Nicholls/File Photo
Talla

Shugaban Hukumar Gudanarwar Kungiyar Tarayyar Turai, Donald Tusk na daga cikin jagogorin kungiyar da suka bayyana shakkunsu kan sabbin kudurorin da gwamnatin Firaminista Boris Johson ta gabatar na ficewa daga EU.

Mr. Tusk ya ce, ya yi ganawar wayar taroho kan batun na Bexit da mahukuntan Dublin da London, yana mai cewa, suna kan bakarsu ta goyon bayan Ireland.

Ana sa ran Mr. Tusk ya jagoranci taron tattaunawa kan batun ficewar Birtaniya da zai gudana a ranar 17 ga wannan wata na Oktoba a birnin Brussels.

Taron wanda zai fayyace makomar ficewar Birtaniya cikin girma da arziki ko akasin haka, za a gudanar da shi ne makawanni biyu gabanin cikar wa’adin ficewar kasar.

Har yanzu dai, batun kan iyakar Ireland ne ke ci gaba da haddasa rashin jituwa tsakanin EU da Birtaniya.

Firaministan Johsnon ya gargadi cewa, muddin kungiyar ta ki amincewa da sabbin kudurirn nasa, to ita ma za a dora mata lafi matsawar kasar ta fice cikin rashin jin dadi nan da karshen watan Oktoba da muke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.