Isa ga babban shafi

'Yan Rasha na zanga-zangar neman sakin 'yan adawar da aka kame

Dubban jama’a sun gudanar da gagarumin gangami a birnin Moscow na Rasha da zummar matsin lamba ga hukumomin kasar don ganin sun saki mutanen da suka cafke sakamakon zanga-zangar adawa da gwamnati da suka gudanar a kwanakin baya.

Dubban Al'ummar na neman ganin lallai gwamnati ta saki mutanen da ta kame yayin zanga-zangar watan jiya da farkon watan nan
Dubban Al'ummar na neman ganin lallai gwamnati ta saki mutanen da ta kame yayin zanga-zangar watan jiya da farkon watan nan REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Jami’an ‘yan sanda sun kiyasta cewa, mutane akalla dubu 20 ne suka fito wannan gangami da aka gudanar a dandalin Sakhorav da ke tsakiyar birnin Moscow kuma sun samu izini daga mahukuntar kasar.

Masu zanga-zangar dauke da alluna na ta rera wake-waken ganin an kawo karshen murkushewar da ake yi wa masu adawa da gwamnatin kasar.

Shugaban ‘yan adawar, Lyubov Sobol ya ce, ya zama wajibi su nemi hakkinsu na ‘yanci, yana mai cewa, ba su da wani zabi face gudanar da zanga-zanga a kan tituna.

Jerin zanga-zangar da aka gudanar a kwanakin baya, sun samo asali ne bayan hukumomin Rasha sun haramta wa Sobol, makusanci ga Alexei Navalvy da ke kan gaba wajen sukar manufofin gwamnatin kasar, tsayawa takara a zaben kananan hukumomi.

Daya daga cikin gangamin da suka fi daukar hankali, shi ne wanda ya samu halartar mutane akalla dubu 50 gabanin zaben na kananan hukomomi, yayin da ‘yan adawar suka lashe gomman kujeru a majalisar dokokin kasar.

A bangare guda, kungiyoyim limaman coci-coci da malaman makarantu sun sanya hannu kan wata budaddiyarc wasika, inda suka nuna goyon bayansu ga ‘yan adawar da aka murkushe, da kuma ake ci gaba da tsare wasunsu a gidan yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.