Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

EU na nadamar gaza wayar da kan 'yan Birtaniya game da Brexit

Shugaban gudanarwar kungiyar kasashen Turai mai barin gado Jean Claude Juncker ya ce har yanzu lokaci bai kure ba na tabbatar da yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga kungiyar ranar 31 ga watan gobe.

Jean Claude Juncker
Jean Claude Juncker REUTERS/Vincent Kessler
Talla

Juncker ya shaidawa Jaridar Spain nadamar sa kan yadda kungiyar Turai bata taka rawa ba wajen magance karairayin da Yan siyasar Birtaniya suka yiwa mutane kafin zaben raba gardamar shekarar 2016.

Jean Claude Juncker ya zargi 'yan siyasar Birtaniya da rufewa 'yan kasar hakikanin abin da shirin ficewar ke nufi.

Shugaban ya bayyana taron da suka yi da Firaminista Boris Johnson makon jiya a matsayin mai muhimmanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.