Isa ga babban shafi
Faransa

Zanga-zanga kan sauyin yanayi ta rikide zuwa tarzoma a Faransa

Zanga-zangar alhini kan matsalar sauyin yanayi da kuma neman hukumomi su gaggauta maganceta, ta juye zuwa tashin hankali a Faransa, abinda ya tilastawa jagororin masu rajin kare muhalli dakatar da tattakin jiya asabar.

Jami'an tsaron Faransa yayin arrangama da masu zanga-zanga.
Jami'an tsaron Faransa yayin arrangama da masu zanga-zanga. AFP / Lucas BARIOULET
Talla

Zanga-zangar lumanar ta rikide zuwa tashin hankali ne, bayan da wasu mutane akalla dubu guda, masu sanye da bakaken riguna, suka shiga cikin masu tattakin, tare da takalar jami’an tsaro, lamarin da ya kai ga kazamar arrangama tsakaninsu.

Zuwa yanzu ‘yan sanda sun kame mutane 163, bayan da tashin hankali yayi sanadin lalata ginin wasu bankuna biyu a Paris, da wasu gidaje dake kusa, sai kuma Babura da dama da aka kone.

Wadanda suka shirya zanga-zangar kan dumamar yanayi a Faransa sun ce mutane dubu 50,000 suka amsa kiransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.