Isa ga babban shafi
Turai

'Yan sanda na tsare da wani mutun da ya kashe matarsa a Faransa

Masu gabatar da kara a Faransa sun ce wani mutum ya kashe matar da suke zama tare a gaban ‘yayan su guda 3, a daidai lokacin da hukumomi ke daukan matakan kawo karshen kisan da ake yiwa mata a kasa.

'Yan sanda a Faransa na aikin sintiri
'Yan sanda a Faransa na aikin sintiri IAN LANGSDON / POOL / AFP
Talla

A wata sanarwa da aka gabatar an gano cewa lamarin ya faru ne a garin Le Havre na kasar Faransa ranar litinin, lokacin da mutumin mai shekaru 37 ya cacakawa matar mai shekaru 27 wuka har sau 14, sakamakon takaddamar rabuwar su, a gaban ‘yayan su masu shekaru 6 da 4 da kuma 2.

Mutumin wanda ya amsa laifin sa, yace yayi haka ne saboda tsoron cewar idan sun rabu matar ba zata bashi damar ganin ‘yayan sa ba.

Daruruwan mutane suka gudanar da zanga zanga jiya domin nuna bacin ran su da kisan, da kuma bukatar hukunta mutumin.

Alkaluma sun nuna cewar, a shekarar bara ta 2018 mata 121 wadanda ke zama da su, ko kuma tsoffin abokan zaman su suka kashe.

Kungiyar dake yaki da cin zarafin mata tace a wannan shekara kawai mata 106 aka kashe a Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.