Isa ga babban shafi
Birtaniya

Ana samun ci gaba a shirin ficewarmu daga Turai- Johnson

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya bayyana cewa ana samun gagarumin cigaba a tattaunawar da kasar ke yi da kungiyar Tarayyar Turai game da shirin ficewarta, inda ya ce suna nan akan bakansu na ballewa daga kungiyar kwatankwacin yadda shirin fina finan Incredibles Hulk ke samun nasara.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson
Firaministan Birtaniya Boris Johnson 路透社。
Talla

Boris Johnson wanda ke wannan batu gabanin ganawarsa da shugabancin gudanarwar kungiyar Tarayyar Turai a yau Litinin ya ce ya na da kwarin gwiwar cimma matsaya a ganawar.

A ganawar ta Johnson da Jean Claude Juncker da kuma Michel Barnier a Lexembourg, sabon Firaministan na Birtaniya zai gabatar kudirinsa game da yarjejeniyar da ya ke fatan cimmawa.

Firaministan yayin ganawarsa da Jaridar Mail a jiya Lahadi, ya ce yana da kyakkyawar fatan kulla yarjejeniya da EU a ranar 17 ga watan Oktoba don bai wa Birtaniyar damar ficewa a ranar 31 ga wata kamar yadda ta ambata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.