Isa ga babban shafi
Faransa

Ma'aikatan sufurin jiragen kasa na yajin aiki a Faransa

Ma’aikatan sufurin jiragen kasa na Kasar Faransa suN tsunduma yajin aiki a Juma'a, domin nuna rashin amincewar su da yunkurin yiwa dokar fansho gyaran fuska.Matakin  ya haifar da cinkoson ababan hawa da kuma tilastawa
 mutane da dama zama a gidajen su.

Fasinjoji da suka  yi dafifi a wata tashar jirgin kasa a Faransa yayin yajin aiki bara.
Fasinjoji da suka yi dafifi a wata tashar jirgin kasa a Faransa yayin yajin aiki bara. REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Rahotanni sun ce an rufe 10 daga cikin layukan dogo 16 a birnin Paris, yayin da aka dakile ayyuka a sauran guda 6.

Daruruwan mutane sun yi dafifi a tashoshin dake aiki musamman lokacin da jama’a suka yi sammako zuwa wuraren ayyukan su.

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace wasu daga cikin jama’a sun koma amfani da kekunan hayar da ake amfani da su domin zuwa wurin aiki.

Yajin aikin shine mafi girma da ma’aikata ke yi domin nuna adawa da shirin shugaba Emmanuel Macron na yi wa dokar fansho gyara domin kawar da kamfanonin dake yiwa kowacce kungiya aiki.

Die Sokhanadu mai shekaru 25 da haihuwa ya shaidawa kamfanin dillancin labaran faransa AFP cewa, shi ma’aikaci ne a majami’ar Notre Dame, kuma ba zai samu karasawa wajen aiki ba, sakamakon yajin aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.