Isa ga babban shafi

Majalisar Turai ta jaddada matsayinta kan ka'idojin fitcewar Burtaniya

Shugabannin Majalisar dokokin kungiyar Turai sun sake jaddada matsayin su na cewa babu wata yarjejeniyar da za’a kulla da Birtaniya na ficewa daga cikin ta ba tare da amincewa da bukatar Ireland ba wadda Firaminista Boris Johnson ke bukatar ganin anyi watsi da shi.

Ursula von der Leyen, zababbiyar shugabar majalisar zartaswar kungiyar tarayyar Turai, kuma ministan tsaron kasar Jamus.
Ursula von der Leyen, zababbiyar shugabar majalisar zartaswar kungiyar tarayyar Turai, kuma ministan tsaron kasar Jamus. REUTERS/Yves Herman
Talla

Yayin da ake cigaba da samun haske na kaiwa ranar 31 ga watan Oktoba ba tare da kulla wata sabuwar yarjejeniya tsakanin Birtaniya da kungiyar Turai ba, shugabannin kungiyar na cigaba da zargin Firaminista Boris Johnson da mayar da hankali kan tattaunawar da bata da kima domin ganin an kai lokacin ba tare da samun mafita ba.

Ana saran Yan Majalisun Turai su kada kuri’ar amincewa da matsayin kungiyar a makon gobe wadda zata mayar da hankali kan dora alhakin duk wata matsalar da za’a samu kan Birtaniya.

Shugaban Majalisar Turai, David Sassoli yace kudirin an makon gobe zai aike da sako karara dake nuna cewar babu yadda Birtaniya zata kulla sabuwar yarjejeniya ba tare da sanya bukatar Ireland ba.

Matsayin Sassoli yayi daidai da na shugaban tawagar masu tattaunawa daga kungiyar Michel Barnier dake cewa idan an kasa kulla yarjejeniyar raba gari, matsalar zata koma kan Birtaniya ne kacaukan.

Yanzu haka wakilin Birtaniya dake jagorancin tattaunawar David Frost ya isa Brussels tun jiya, inda zai gana da wakilan Turai zuwa gobe juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.