Isa ga babban shafi

Matakin Johnson na kulle Majalisa ya sabawa doka- Kotu

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya sake shan sabon kaye a yau Laraba, bayan da wata kotu a Scotland ta yanke hukucin kan matakinsa na dakatar da Majalisar Dokokin kasar wanda ta bayyana a matsayin abin da ya sabawa doka.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson
Firaministan Birtaniya Boris Johnson REUTERS/Phil Noble
Talla

Bayan wannan hukunci na kotu ne Jam’iyyar adawa ta Labour ta bukaci Johnson ya gaggauta bude Majalisar Dokokin kasar, wanda ya dakatar na makonni biyar a jiya Talata.

Sai dai kuma yanke hukuncin kotun ke da wuya gwamnatin Biryaniyar ta daukaka  kara nan ta ke, yayinda aka sanya ranar Talata mai zuwa a matsayin ranar fara sauraron shari'ar, yayinda Majalisar dokokin za ta ci gaba da kasancewa a rufe.

Johnson dai ya ce matakin rufe Majalisar Dokoki har zuwa 14 ga watan Oktoba ba bakon abu bane, an yi haka ne don bai wa gwamnati sukunin kaddamar da wasu manufofin majalisar.

Amma masu suka sun zargi Johnson da kokarin rike wa ‘yan adawa a majalisar mara, don ya aiwatar da barazanar sa na ficewa daga Tarayyar Turai ko da yarjejiya ko babu a ranar 31 ga watan Oktoba.

Wata karamar kotun Scotland ta yi watsi da korafin da wasu ‘yan majalisa su 78 suka shigar gabanta a makon da ya gabata, amma kotun koli ta yi watsi da hukuncin a Laraban nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.